Daga Mubarak Ibrahim Mandawari
Ƙungiyar ɗaliban Najeriya ta ƙasa {NANS} ta ba gwamnatin tarayya wa’adin mako biyu da ta ceto wasu ɗaliban koyan aikin likita su ashirin, da ƴan bindiga suka yi garkuwa da su a jihar Binuwai.
Shugaban ƙungiyar ɗaliban Najeriya, Muhammad Sabo ya shaida wa manema labarai cewa a wannan karon ƙungiyar baza ta zuba ido taga ana cutar da ɗaliban ba.
Ya ƙara da cewa gaza ceto ɗaliban zai sa a ga fushin su fiye da yadda aka saba gani.
Wannan dai ba shine karon farko da ake sace ko kuma garkuwa da ɗaliban ƙasar ba, a hanyar su ta komawa gida ko kuma a cikin ɗakunan kwanansu dake cikin makarantu.
Jihar Zamfara sun fuskanci irin wannan matsalolin a baya.
Ɗalibai masu shirin bautar ƙasa suma basu tsira daga ayyukan ƴan bindigan ba,a baya an yi dasu a kan hanyoyin su na shiga dandalin horas da ƴan hidimtawa ƙasa, musamman a hanyoyin sakkwato, Zamfara da Kebbi.
Ɗaliban ƙasar sun fuskanci matsaloli da suka haɗa da yajin aiki kashi-kashi, harda wanda aka shafe watanni shida wanda hakan ya tsayar da karatunsu baki ɗaya.