Gwamnatin Najeriya ta ayyana ranar Litinin 16 ga watan Satumba, a matsayin ranar hutu ga ma’aikatan ƙasar, domin bikin ranar Maulidin Annabi Muhammad S.A.W.
Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da babban sakatare a ma’aikatar cikin gida ta Najeriya, Dokta Magdalene Ajani ya fitar.
Ya ce ministan ma’aikatar, Dakta Olubunmi Tunji-Ojo, ne ya bayyana hutun Maulidin a madadin gwamnatin Najeriya.
Sanarwar ta ce, ”Gwamnatin Najeriya na taya al’ummar Musulmin ciki da na waje murnar zagayowar ranar Maulidin”
Ministan ya yi kira ga musulman Najeriya su yi amfani da lokacin bikin Maulidin wajen yi wa ƙasar addu’ar zaman lafiya da ci gaba.