Gwamnatin Najeriya ta sanar da cewa a gobe Lahadi Matatar man fetur ta Dangote za ta soma rarraba tataccen man fetur a faɗin ƙasar.
Shugaban Hukumar Tattara Kudaden Shiga (FIRS), Dokta Zacch Adeji ne ya bayyanawa Ministan Kudi Wale Edun yayin wani taron manema labarai ranar Juma’a a Abuja.
A jawabin na Dokta Zacch an tabbatar da cewa Kamfanin Man Fetur na Najeriya NNPCL ne zai dauki ragamar rarraba man da Matatar Dangote ke tacewa ga dillalan man kasar.
Matatar Dangote dai na tace danyen mai da ya kai yawan ganga dubu dari shida da hamsin a duk rana, lamarin da ya kawo karshen takaddamar da aka jima ana fuskanta kan batun rarraba man.
Ministan ya ce a gobe Lahadi NNPCL zai fara sayen man daga Matatar Dangote sannan ya rika sayar wa ’yan kasuwa a fadin kasar.
Jama’ar Najeriya na fama da karancin man fetur a fadin kasar, a daidai lokacin da tsadarsa ke ci gaba da jefa jama’a cikin mawuyacin hali na kangin rayuwa.