Ministan yaɗa labarai da wayar da kan al’umma a Najeriya Mohammed Idris Malagi ya yi kira ga ‘yan jarida a ƙasar nan su riƙa aiki a bisa doron doka da oda.
Yayin jawabin buɗe taron, Shugaban Hukumar Kula da Gidajen Jarida a Najeriya (Nigeria Press Council) Dokta Dili Ezughah, da ya wakilci ya jaddada muhimmancin kafafen yaɗa Labarai wajen wayar da kan al’umma.
Mimistan ya yi kira ga kafafen yaɗa labarai da su dinga gabatar da ayyukansu kamar yadda doka ta bayyana.
Ya kuma yi kira ga kafafen Yada Labarai da su mara wa Gwamnatin tarayya baya wajen sanar da al’umma kyawawan manufofinta.
- Yadda ‘Yan Arewa Suka Ba Tinubu Mulkin Najeriya—Reno Omokri
- Najeriya Sabon Jini Take Buƙata ~ Obasanjo
Ministan ya ce, gwamnatin Bola Ahmed Tinibu a shirye take tayi aiki da wannan ƙungiya wajen wayarda kan al’umma.
Dokta Dili Ezughah ya ce ministan ya taya ƙungiyar murnar gabatar da taron ta na farko da zaben Kungiyar cikin ɗan kankanin locaci.
A nasa jawabin Shugaban gidan Talabijin na Kasa Kuma Mai masaukin baki, Kwamared Salihu Abdulhamid Dembos Ya bayyana muhommanci taron, in da ya ce za’a gabatar da makaloli akan ci gaba da kuma kalubalen da kafafen yaɗa Labarai ke fuskanta a wannan karnin.
Daraktar Kungiyar na Kasa Kuma Sekataren zartarwa kuma Shugaban gidajen yada Labarai na Nigeria, Dr. Yemisi Bamgbose, ya tabo kadan daga cikin tarihin Kungiyar wacce ta samu asali tun 1962 amma sai yanzu aka farfado da ita.