Shahararren mai amfani da kafafen sada zumunta, Reno Omokri ya ce ‘yan Arewacin Najeriya, musamman arewa maso yammaci ne suka bai wa shugaba Bola Ahmed Tinubu mulkin ƙasar nan.
Reno ya yi wannan bayani biyo bayan wasu rubuce-rubuce da wasu ke yi ka cewa ‘yan arewa sun fito zanga-zanga ne domin su kifar da gwamnatin Tinubu.
Ya ce, idan uwa na son kashe ɗanta, ba sai ya girma za ta nemi kashe shi ba, tun yana tsumma za ta halaka shi cikin ruwan sanyi.
Reno ya ce, da ‘yan Arewacin Najeriya ba su ga dama ba, da babu yadda Tinubu zai yi ya zama shugaban Najeriya.
A bayanin nasa ya ce, Kafin zaben fidda gwani, Gwamnonin APC na Arewa sun yi taro a Abuja ranar 6 ga watan Yuni, 2022, inda suka ce duk da cewa su na da ikon fitar da ɗan takarar shugaban kasa daga yankin Arewa a jam’iyyar APC, don neman hadin kan Najeriya, sun yarda ɗan takarar shugaban ƙasa ya fito daga Kudu.
Wannan amincewar da gwamnonin Arewa na jam’iyyar APC su ka yi, itace ta baiwa Bola Ahmed Tinubu damar zama ɗan takara.
Sakamakon zaɓe.
Daga cikin kuri’u miliyan 8 da dubu ɗari 794 da ɗari 726 da Bola Tinubu ya samu , miliyan 5 da dubu ɗari 602 da ɗari 682 daga daga Arewa ya samo su.
Sai ya samo kuri’a miliyan biyu 2 da dubu ɗari 279 da ɗari 407 kacal daga Kudu maso Yamma wato yankin da ya fito.
Sa’annan ya samo wasu ƙuri’u miliyan 1 da dubu ɗari 207 da ɗari 370 daga Kudu maso Gabas.
A takaice dai, Arewa ce ta sa Bola Tinubu ya zama Shugaban ƙasa a yau, musamman ma Arewa maso Yamma, inda ta bashi ƙuri’a miliyan 2 da dubu ɗari 652 da ɗari 235.