Home » An ceto wasu cikin ɗaliban Gusau da aka sace

An ceto wasu cikin ɗaliban Gusau da aka sace

by Anas Dansalma
0 comment
Yan bindiga

An yi nasarar ceto shida daga cikin ɗaliban Jami’ar Tarayya da ke Gusau waɗanda ƴan bindiga suka yi garkuwa da su daren Juma’a.

Sai dai har yanzu babu tabbas kan yawan ɗaliban da maharan suka sace.Ƴan bindigar sun isa unguwar Sabon Gida da tsakar dare, sun rinƙa harbe-harbe kafin su yi awon-gaba da ɗaliban.

Jami’in hulɗa da jama’a na jami’ar, Umar Usman ya tabbatar da faruwar lamarin, sai dai bai bayyana adadin ɗaliban da aka yi garkuwar da su ba.

Zamfara na daga cikin jihohin da suka fi jigata daga ayyukan ƴan bindiga masu fashi da kuma garkuwa da mutane domin neman kuɗin fansa.

Ko a cikin watan Fabarairun 2021, ƴan bindiga sun shiga makarantar sakandare ta GGSS Jangebe a jihar, inda suka sace ɗalibai mata 317.

Haka nan ma a baya-bayan nan ƴan bindiga sun kai hari a wasu ƙauyukan jihar inda suka kashe mutane da dama tare da sace ƴan mata fiye da 30 a ƙaramar hukumar Maradun.

Gwamnatin jihar Zamfara ƙarƙashin gwamna Dauda Lawal, ta ce tana ɗaukar duk matakan da suka dace wajen shawo kan lamarin, sai dai ta sha alwashin cewa ba za ta taɓa yin sulhu da ƴan bindiga ba.

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai dake da cikakkiyar rejista da ke da manufa ta ilimantarwa, wayar da kai Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.

Ofishinmu yana nan a kan titin Guda Abdullahi dake Farm Centre a jihar Kano. 

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi