Home » An Dage Jana’izar Aminu Ɗantata Zuwa Talata

An Dage Jana’izar Aminu Ɗantata Zuwa Talata

by Mujahid Wada Guringawa
0 comment

Gwamnatin Najeriya ta sanar da ɗage jana’izar fitaccen ɗankasuwar nan, Alhaji Aminu Dantata da ya rasu ranar Asabar a ƙasar Hadaɗɗiyar Daular Larabawa.

Ministan yaɗa labaran Najeriya, Mohammed Idris ya tabbatar wa da BBC ɗage jana’izar sakamakon rashin isar gawar marigayin a kan lokaci zuwa birnin Madina.

”Akwai ƙa’idoji da gwamnatin Saudiyya ta shimfiɗa kan yadda za a shigar da gawa domin yi mata jana’iza a ƙasar, to yanzu haka ana nan ana ta cike-ciken takardu tsakanin gwamnatin Saudiyya da iyalan mamacin,”in ji ministan.

Mohammed Idris ya ce idan an kammala za a ɗauko gawar daga Hadaɗɗiyar Daular Larabawa zuwa Saudiyya.

Ya ƙara da cewa tuni ofishin jakadancin Najeriya a Saudiyya da iyalan mamacin suka kammala shirye-shiryen jana’izar.

Bayanai sun ce Alhaji Aminu Ɗantata ne ya bar wasiyyar binne shi a birnin Madina, garin Manzon Allah, burin da hukumomin Saudiyya suka amince da shi.

Tuni dai tawagar da gwamnatin Najeriya ta tura zuwa Madina na ƙasar Saudiyya domin halartar jana’izar Alhaji Aminu Ɗantata ta isa ƙasar.

Tawagar gwamnatin tarayyar ƙarƙashin jagorancin ministan tsaron ƙasar, tsohon gwamnan Jihar Jigawa, Alhaji Muhammad Badaru Abubakar.

Sauran mambobin tawagar sun haɗa da ministan shari’a kuma babban lauyan gwamnatin tarayya, Lateef Fagbemi (SAN) da ministan yaɗa labarai, Alhaji Mohammed Idris, da ƙaramin ministan gidaje da raya birane, Hon. Yusuf Abdullahi Ata da dai sauran su.

Akwai kuma manyan malamai a cikin tawagar da suka haɗa da sheikh Aminu Daurawa da Dr Bashir Aliyu Umar da kuma Khalifa Abdullahi Muhammad.

Shi ma Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya jagoranci wata babbar tawaga zuwa birnin na Madina tare da Sarkin Kano, Khalifa Muhammadu Sanusi II da gwamnan Jihar Jigawa, Alhaji Umar Namadi, da tsohon gwamnan Jigawa, Barista Ali Sa’ad Birnin Kudu, da sauran manyan jami’an gwamnati da dattawan jihar Kano.

Marigayi Aminu Dantata, wanda ya shahara wajen kasuwanci da sadaka da hidimar jama’a, ya rasu ne a Abu Dhabi, babban birnin Hadaddiyar Daular Larabawa.

“Mutuwarsa ta bar giɓi a harkokin tattalin arziki da walwalar al’umma, tare da kammala wani babi mai muhimmanci a tarihin Najeriya,” in ji sanarwar gwamnatin

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai mai cikakkiyar rajista wadda manufarta ita ce ilimantarwa, da wayar da kai da Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.
Muna nan a kan titin Guda Abdullahi gida mai lamba 19 a Farm Centre, jihar Kano.

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi

©MuhasaTVR 2023. Ku nemi izini kafin yin amfani da duk abin da aka wallafa a wannan shafi

Are you sure want to unlock this post?
Unlock left : 0
Are you sure want to cancel subscription?