A yayinda ya rage kwana ɗaya wasu ‘yan Najeriya su fara Zanga-zangar adawa da yunwa da tsadar rayuwa, Gwamnatin tarayya ta ce ta karye farashin shinkafa zuwa Naira dubu arba’in.
Gwamnatin Najeriya ta ce ta tanadi wani adadi mai yawa na manyan buhunan shinkafar da za a sayar a sassan kasar da nufin samar da sauki ga jama’ar ta.
A halin da ake cika dai a kasuwanni ana sayar da babban buhun shinkafar ne kusan naira dubu 80, wannan tsadar na ɗaya daga cikin manyan dalilan da suka sa wasu ƴan Najeriya shirin gudanar da zanga-zanga domin nuna fushinsu.
Ministan yada labarai Muhammad Idris ne ya shaida wa ‘yan jarida cewa, gwamnatin tarayya ta karya farashin shinkafar zuwa naira dubu 40 kan duk buhu daya mai nauyin kilogiram 50.
- APC Ta Zargi Masu Zanga-zanga Da Niyyar Kifar Da Gwamnatin Tinubu
- Majalisa Za Ta Yi Zaman Gaggawa Saboda Zanga-zanga
Muhammad Idris ya ce, an ware wurare na musamman da za a sayar da shinkafar a sassan jihohin Najeriya.
Sai dai kawo yanzu, gwamnatin ba ta bayyana wuri da lokacin da za ta fara sayar da shinkafar a farashin da ta bayyana ba.
Muhammad Idris ya ce suna kyautata zaton idan aka ci gaba da kawo matakai irin waɗannan, sannu a hankali abubuwa za su yi sauƙi.