Ƙungiyar Tuntuba Ta Arewa ta dakatar da shugabanta na kasa, Mamman Mike Osuman, sakamakon kalamansa dangane da zaben 2027 da ke tafe.
An ruwaito shugaban da aka dakatar a yayin taron majalisar zartaswar kungiyar ACF ta kasa a ranar Larabar da ta gabata yana cewa Arewa za ta marawa dan takarar shugaban kasa da ya fito daga arewa baya, a zaben 2027 idan Allah ya kai mu.
Sai dai a wata sanarwa da kungiyar ta fitar a ranar Alhamis ta bakin shugaban kwamitin amintattunta Alhaji Bashir Dalhatu Wazirin Dutse da babban sakatarenta Murtala Aliyu, kungiyar ta ce Osuman ya bayyana hakan ne ba tare da tuntuba ko tattaunawa da wasu shugabanni da mambobin kungiyar ta ACF ba, don haka abin da ya faɗa ra’ayinsa ne na ƙashin kai ba na ƙungiyar ba.
Domin haka ACF, ta sanar da dakatar da Osuman a matsayin shugaban ƙungiyar nan take, sannan ta kafa kwamitin da zai binciki abin daya faru.