Wasu ’yan mata biyar sun yi nasarar gudowa daga hannun ’yan ta’addan Boko Haram a Karamar Hukumar Gwoza Jihar Borno.
Rundunar Sojojin Operation Hadin Kai ta ce ta ceto ’yan matan ne a ranar 4 ga Yuni yayin da ake ci gaba da sintiri da hare-hare a yankin Arewa maso Gabas.
Ta bayyana cewa sojojin bataliya ta 82 sun ceto Aisha Idrisa mai shekara 13 da Fatima Abubakar mai shekara 11 a kusa da yankin Amuda da ke Karamar Hukumar Gwoza.
An ce sun tsere daga yankin Sahalawa bayan hare-haren bama-bamai da sojoji suka kai, wanda ya tilasta wa ’yan ta’addan barin wuraren da suka mamaye.\
Bayanan farko sun nuna cewa ’yan matan ’yan asalin yankin Pulka ne, kuma an sace su tun shekarar 2025. Daga baya an tantance su, an rubuta bayanansu sannan aka haɗa su da iyalansu a sansanin ’yan gudun hijira na Pulka.
Sauran ’yan mata uku kuma sun miƙa kansu ga sojojin rundunar 26 Task Force Brigade da ke Gwoza bayan sun tsere daga Guduf Nagadayo a tsaunukan Mandara.
Sojojin sun ce ana ci gaba da gwaje-gwaje da tantance bayanansu bisa ƙa’idojin da aka kafa.
’Yan matan da suka gudo sun hada da Wuriya Kaka mai shekara 12 da Fauza Abu mai shekara 13, da kuma Hussaina Usman mai shekara 13.
Masu sharhi kan tsaro sun bayyana cewa ƙaruwar waɗanda ke tserewa daga wuraren da ’yan ta’adda ke riƙe da su na nuna tsaninin matsin lambar da ƙungiyoyin ta’addanci ke fuskantar daga hare-haren soji a Arewa maso gabas.
Sojojin sun kara da cewa yanayin tsaro da kwanciyar hankali a yankin ya fai yadda yake a baya, duk da cewa ba za a iya hasashen gaba ba.
Rundunar ta ce za ta ci gaba da nuna ƙwazo da ƙwarin gwiwa a yaƙin da take yi da ta’addanci.
