Gwamnatin Jihar Kano ta tabbatar da dakatar da wasu yan Jarida 14 daga ɗaukar rahotanni a fadar Gwamnatin Jihar.
Mai magana da yawun gwamnan jihar Kano Sanusi Bature Dawakin Tofa ne ya sanar da hakan cikin wata buɗaɗɗiyar wasiƙa da ya fitar.
Duk da cewa babu wani dalili da aka bayyana na dakatar da su ɗin, saƙon da aka tura a cikin guruf na WhatsApp ɗin masu yaɗa labarai ya yi kira a gare su da su yi biyayya ga umarnin wanda zai fa ra aiki a yau Talata.
Jerin ‘yan jarida da aka dakatar sun haɗa da Aliyu Yusuf, Sani Suraj Abubakar da Adamu Dabo da Naziru Ya’u da Sadiq Sani AA da Umar Sheka da Simon Da Nasiru Danhaki da Abdullahi Suke da Murtala Baba Ƙusa da Ibrahim Mu’azzam
“Ana saka ran sunayen da aka ambata za su komawa guraren aikin su don cigaba da sauran ayyuka.” a cewar Bature.