Home » An Daure Barawon Waya Shekaru 2 A Kano 

An Daure Barawon Waya Shekaru 2 A Kano 

by Muhammad Auwal Suleiman
0 comment

Kotun Shari’ar Musulunci da ke Fagge ’Yan Alluna a Jihar Kano, ta yanke wa wani matashi hukuncin ɗaurin shekara biyu, a gidan yari bayan samun sa da laifin satar wayoyin salula.

An gurfanar da Aliyu Rabi’u Rijiyar Lemo a gaban kotun, bayan kama shi a kan titin Ibrahim Taiwo tare da wasu biyu, inda suke amfani da Adaidaita Sahu wajen satar wayoyin hannun fasinjoji.

A wajen da aka kama shi, wasu fusatattun mtsne sun ƙone Adaidata Sahun da suke amfani da shi wajen aikata laifin.

An tuhume shi da haɗa baki don aikata laifi, sata, da tayar da hankalin jama’a.

Matashin ya amsa laifukan nan gaba ɗaya.

Alƙalin kotun, Khadi Umar Lawan Abubakar, ya yanke masa hukuncin watanni shida a gidan yari ko kuma ya biya tarar Naira 20,000 kan laifin haɗa baki.

Ɗaurin shekara ɗaya a gidan yari kan satar waya, da kuma wata shekara ɗaya kan tayar wa jama’a hankali, ba tare da zaɓin biyan tara ba.

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai mai cikakkiyar rajista wadda manufarta ita ce ilimantarwa, da wayar da kai da Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.
Muna nan a kan titin Guda Abdullahi gida mai lamba 19 a Farm Centre, jihar Kano.

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi

©MuhasaTVR 2023. Ku nemi izini kafin yin amfani da duk abin da aka wallafa a wannan shafi

Are you sure want to unlock this post?
Unlock left : 0
Are you sure want to cancel subscription?