Home » ’Yan Bindiga Sun Sace Budurwa Bayan Karbar Kudin Fansa

’Yan Bindiga Sun Sace Budurwa Bayan Karbar Kudin Fansa

by Muhammad Auwal Suleiman
0 comment

’Yan bindiga sun kai hari Garo da ke Ƙaramar Hukumar Kabo a Jihar Kano cikin daren ranar Lahadi, inda suka sace wata budurwa mai suna Zainab Auwalu, bayan sun karɓi kuɗin fansa Naira miliyan takwas daga hannun mahaifinta.

Zainab, wadda ta kammala makarantar sakandare kwanan nan, an sace ta a gidan mahaifinta, Alhaji Auwalu.

Shaidu sun bayyana cewa ’yan bindigar, kimanin su 10, sun shiga garin da babura ɗauke da muggan makamai.

Sun shiga gidan Alhaji Auwalu da misalin ƙarfe 1:30 na dare, inda suka shafe awanni suna cin karensu ba babbaka, sannan suka tafi da kuɗin fansa tare da sacw ‘yarss.

Wani mazaunin garin, Haruna Muhammad, ya ce harin ya jefa al’ummar garin cikin firgici.

Mutane da yawa na zargin cewa wasu mazauna garin ne suka bai wa ’yan bindigar bayanai.

Kakakin ’yan sandan jihar, Abdullahi Haruna Kiyawa, ya tabbatar da faruwar lamarin.

Ya bayyana cewa jami’an tsaro na ƙoƙarin bin sahun ’yan bindigar da kuma ceto matashiyar.

Ko da yake satar mutane da fashi ba su yawaita a Jihar Kano ba, garuruwa irin su Garo da sauran yankunan Arewacin Kano da ke kusa da jihohin Kaduna da Katsina, sun sha fuskantar hare-haren ’yan bindiga. Kamar yadda jaridar Aminiya ta wallafa. 

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai mai cikakkiyar rajista wadda manufarta ita ce ilimantarwa, da wayar da kai da Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.
Muna nan a kan titin Guda Abdullahi gida mai lamba 19 a Farm Centre, jihar Kano.

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi

©MuhasaTVR 2023. Ku nemi izini kafin yin amfani da duk abin da aka wallafa a wannan shafi

Are you sure want to unlock this post?
Unlock left : 0
Are you sure want to cancel subscription?