Home » An Gurfanar Da Shamsiyya Da Tawagar Ta

An Gurfanar Da Shamsiyya Da Tawagar Ta

by Muhammad Auwal Suleiman
0 comment

Daga: Mujahid Wada Musa

Rundunar ‘yan sandan Jihar Kano, ta bayyana cewa ta gurfanar da Shamsiya Adamu a gaban kotu bayan sake kama karin mutane 4 da kwato wayoyin sata 12 da ake zargin suna cikin gungun mutanen da  ta ke jagoranta wurin sata da damfarar jama’a.

Kakakin rundunar yan sandan Jihar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya aikewa da manema labarai a ranar Talata.

A ranar 2 ga watan Janairun 2025, rundunar ‘yan sandan Kanon, ta yi holen matashiyar mai suna Shamsiyya da ake zargi da ƙwarewa wajen satar wayoyi a unguwanni daban-daban a sassan Jihar, bayan shafe shekara guda ana farautar ta.

”Shamsiyya ta ƙware wajen ɓullo da dabarun yaudara daban-daban don ilata mutane wajen sace musu wayoyi”.

Kiyawa ya ƙara da cewa wadda ake zargin na yi aiki tare da wasu mutu huɗu da ke taimaka mata ciki har da ɗan adaidaita sahu da mai cire musu kudi a cikin wayoyin da suka sata.

”Ƙwararriyar mai yaudara ce da ke shiga gidajen matan aure tare da sace musu wayoyinsu da kuma yin amfani da wayoyin wajen sace musu kuɗaɗen daga asusun ajiyarsu na banki.

Tuni dai aka gurfanar da Shamsiyya, da kuma gungun matasan da aka kama su tare bisa zarginsu da hada kai da shiga ta laifi da kuma sata , a gaban kotun majistiri mai lamba 18 dake zamanta a Gyadi-gyadi, inda kotun ta bayar da umarnin a tsare su a gidan ajiya da gyaran hali da tarbiya.

Karin mutane hudun rundunar yan san ta sake kamawa sun hada da Fati Auwal, Kamal Sale, Usman Nasir da kuma Bashir Ibrahim, da yanzu haka suke hannun jami’an yan sanda don gudnar da bincike bisa zarginsu da aikata sata da kuma siyan kayan sata.

SP Abdullahi Kiyawa, ya kara da cewa sun karbi korafe-korafen mutane 86 kan gungun mutanen da suke satar wayoyin al’ummar musamman a gidajen mata aure da kuma wuraren sana’o’insu.

A karshe Kiyawa ya ce, kwamishinan yan sandan Jahar CP Salman Dogo Garba, ya bayar da umarnin ci gaba da fadada bincike don dawo da sauran wayoyin salular da aka sace.

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai mai cikakkiyar rajista wadda manufarta ita ce ilimantarwa, da wayar da kai da Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.
Muna nan a kan titin Guda Abdullahi gida mai lamba 19 a Farm Centre, jihar Kano.

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi

©MuhasaTVR 2023. Ku nemi izini kafin yin amfani da duk abin da aka wallafa a wannan shafi

Are you sure want to unlock this post?
Unlock left : 0
Are you sure want to cancel subscription?