Home » Gwamnatin Kano Za Ta Hada Guiwa Da IDB Domin Samar Da Makarantu

Gwamnatin Kano Za Ta Hada Guiwa Da IDB Domin Samar Da Makarantu

by Muhammad Auwal Suleiman
0 comment

Gwamnatin jihar Kano ta kaddamar da shirin hada gwiwa da Bankin Raya Kasashen Musulmi  (IDB) domin samar da makarantu guda hudu da za a rika koyarwa da harshen  Ingilishi da kuma Larabci.

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana hakan ne a lokacin kaddamar da raba kayan makaranta guda dubu 789,000 ga dalibai a makarantun gwamnati dubu 7,092 dake fadin kananan hukumomin Kano 44.

Gwamna Abba ya ce wannan gagarumin shiri na daga cikin kokarin shigar Almajirai tsarin karatun boko da kuma rage adadin yaran da ba sa zuwa makaranta a jihar.

Gwamnan ya bayyana nasarori da dama a karkashin dokar ta baci da gwamnatinsa ta saka a fannin ilimi, wanda ya kai ga gina sabbin ajujuwa guda 336, da gyara wasu 119 da suka lalace, tare da samar da sama da tebura da kujeru 3, 53,000. kashi na farko.

Ana sa ran za a dauki dalibai sama da 160,000 a wadannan makarantu idan aka bude su domin amfanin al’umar jihar Kano. 

Bugu da kari, an raba litattafai sama da miliyan daya da dubu dari uku, inda ‘yan mata dubu 45,000 suka ci gajiyar tallafin kudin karatu na Naira 20,000 kowannensu.

Gwamna Yusuf ya tabbatar wa al’ummar Kano cewa gwamnatinsa ta himmatu wajen farfado da harkar ilimi.

Gwamnan ya kuma nuna jin dadinsa ga al’ummar Kano bisa ci gaba da goyon bayan da suke ba shi, ya kuma yi alkawarin samar da karin ayyukan kawo sauyi a fannoni da dama.

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai mai cikakkiyar rajista wadda manufarta ita ce ilimantarwa, da wayar da kai da Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.
Muna nan a kan titin Guda Abdullahi gida mai lamba 19 a Farm Centre, jihar Kano.

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi

©MuhasaTVR 2023. Ku nemi izini kafin yin amfani da duk abin da aka wallafa a wannan shafi

Are you sure want to unlock this post?
Unlock left : 0
Are you sure want to cancel subscription?