Home » An Halaka Wani Ƙasurgumin Ɗan Ta’adda Da Yaransa A Zamfara

An Halaka Wani Ƙasurgumin Ɗan Ta’adda Da Yaransa A Zamfara

by Muhammad Auwal Suleiman
0 comment
zamfara

Rundunar ’yan sandan Jihar Zamfara ta kashe wani ƙasurgumin ɗan bindiga da ake kira Ɗan Mudale da ya addabi mazauna yankin Tsafe da yankunan dake makwabtaka.

Rundunar ta ce a ranar Alhamis ne ta daƙile wani harin ’yan bindiga a ƙauyen Keta da ke Ƙaramar Hukumar Tsafe.

Wannan bayani na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da kakakin rundunar, DSP Yazid Abubakar ya fitar a Gusau, babban birnin jihar Zamfara.

DSP Yazid ya ce, a yayin daƙile harin ne ’yan sanda suka kashe gomman ’yan bindigar ciki har da Ɗan Mudale wanda ya addabi al’ummar yankin da taaddanci.

Ya ce rundunar haɗin gwiwa da ta haɗa da ’yan sanda da askarawa da kuma mafarauta ce ta yi karon batta da ’yan ta’addar da aka riƙa musayar wuta har aka yi nasara.

Sai dai ya bayyana takaicin cewa wani jami’in ɗan sanda daya da askarawa huɗu da kuma wasu mafarauta sun sadaukar da rayukansu a yayin artabun.

Sanarwar ta ce a halin yanzu wasu mafarauta biyu na karɓar magani a Cibiyar Lafiya ta Tarayya da ke Gusau.

Kazalika, rundunar ’yan sandan ta ƙara jaddada ƙudirinta na tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar.

Ta yi kira ga mazauna da su riƙa gaggauta miƙa mata rahoton duk wani motsi da su aminta da shi ba domin a ɗauki matakin da ya dace.

Mutuwar Ɗan Mudale ne zuwa bayan kashe Kachalla Isuhu Yellow, wani ƙasurgumin ɗan bindiga da ke sahun waɗanda suka jagoranci kitsa harin da aka kai jirgin ƙasan Kaduna zuwa Abuja shekaru biyu da suka gabata.

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai mai cikakkiyar rajista wadda manufarta ita ce ilimantarwa, da wayar da kai da Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.
Muna nan a kan titin Guda Abdullahi gida mai lamba 19 a Farm Centre, jihar Kano.

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi

©MuhasaTVR 2023. Ku nemi izini kafin yin amfani da duk abin da aka wallafa a wannan shafi

Are you sure want to unlock this post?
Unlock left : 0
Are you sure want to cancel subscription?