Daga: Mujahid Wada Musa
Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta samu nasarar kama wasu mutane 6 da ake zargin sun addabi sassan birnin da sace-sacen wayoyin fasinjoji, tare da kwato baburan adaidaita sahu 2 da kuma wayoyin sata 15.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar yan sandan jihar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a daren Alhamis.
Sanarwar ta ce an kama waɗanda ake zargin ne daga ranar 11 zuwa 15 ga watan Janairun 2025, bayan samun bayanan sirri kan maɓoyar ɓatagarin a sassan birnin Kano.
Waɗanda ake zargin sun haɗa da, Bashir Isah, Isyaku Bala, Mudansir Ayuba, Muzambil Abdullahi, Ibrahim Mohammed da kuma Hassan Sagir.
SP Kiyawa ya ƙara da cewa, dukkan waɗanda ake zargin sun amsa laifinsu da cewa sun ƙware wajen satar wayoyin fasinjojin da suke dauka a baburansu na adaidaita sahu.
Baburan guda biyu suna ɗauke da lambar , KBT-850WZ da kuma DAL-113WZ sai wayoyin salula 15 da rundunar ta ƙwato daga hannunsu.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano, CP Salman Dogo garba, ya yaba wa jami’ansa bisa ƙwarewar da suka nuna yayin kai sumamen kamo waɗanda ake zargin tare da yin kira ga al’umma su ci gaba da ba su haɗin kai .
A ƙarshe rundunar ta bayyana cewa duk wanda ya gane wayarsa ko baburin adaidaita sahu cikin kayan da rundunar ta kama ya garzaya ofishin kakakin rundunar ‘yan sandan Kano, don yin ƙarin haske.