Rundunar ‘yan sandan Najeriya sun cafke wata budurwa ‘yar kimanin shekaru 15 da wasu mutane 5 kan zargin safarar miyagun kwayoyi a jihar Delta.
Mai magana da yawun rundunar Bright Edafe ya ce sun samj wannan nasara ce a wani yunukuri na kakkabe masu wannan mummunan sana’a a fadin jihar.
Edafe ya ce za a mika wadan da ake zargin gaban alkali da zarar sun kammala bincikensu
