Daga: Safiyanu Haruna Kutama
Gwamnatin jihar Kano ta amince da ranar juma’a 28 ga watan fabarairu, 2025, a matsayin ranar hutun Zango karatu na biyu ga makarantun firamare da sakandire dake jihar baki daya.
A wata sanarwa da daraktan wayar da kan al’umma na ma’aikatar ilimi ta jihar Kano, Balarabe Abdullahi Kiru ya aikewa manema labarai , ya ce hutun ya shafi makarantu masu zaman kansu da na gwamnati .
Sanarwar ta ce daliban makarantun firamare da sakandire na kwana za su koma Makarantunsu a ranar lahadi 06 ga watan Afirilu,2025, su kuma na makarantun jeka ka dawo za su koma Makarantar ranar litinin 07 ga watan Afirilu, 2025.Kwamishinan ilimi na jihar Kano Dr. Ali Haruna Makoda ya bukaci iyayen yaran da su tabbatar da cewa ya’yansu sun koma Makarantar a ranakun da aka sanya.
Sanarwar ta gargadi masu makarantu masu zaman kasansu da su tabbatar da bin ka’idar da aka gindaya ko kuma su fuskanci hukunci.