Rundunar ’Yan Sandan Jihar Yobe, ta kama wasu mutum biyu da ake zargi da hannu a kisan wani manomi a Ƙaramar Hukumar Bursari, tare da ceto wani yaro mai shekaru tara da ake zargin an tsare shi na tsawon wata huɗu a Ƙaramar Hukumar Jakusko.
Kakakin rundunar, ASP Yusuf Adamu Ali ne, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a.
Ya ce a ranar 30 ga watan Satumba, 2026, rundunar ta samu rahoton gano gawar wani mutum da ba a san ko wane ne ba a wani daji da ke kusa da ƙauyen Rini-Kunu, a Ƙaramar Hukumar Bursari.
A cewar rundunar, jami’an ’yan sanda sun isa wajen nan take tare da kai gawar zuwa Asibitin Ƙwararru da ke Gashuwa, inda likita ya tabbatar da mutuwar mutumin.
Daga baya an gano mamacin mai suna Inusa Abdullahi wanda manomi daga Ƙaramar Hukumar Kazaure ta Jihar Jigawa.
Bincike ya nuna cewa wani mazaunin Rini-Kunu, mai suna Audu Auta, ya zargi mamacin da satar janareta na famfon ruwa.
An ce Audu ya kai zargin gaban wani Malam Muhammad Ibrahim, wanda ake zargin ɗan banga ne, inda shi da wani Abubakar Bulama suka kama mamacin suka kai shi gona.
Rahoton ya ce an tsare mamacin tare da azabtar da shi, inda daga baya aka gano cewa ya mutu.
Ana zargin mutanen biyu da jefar da gawarsa a cikin dajin.
Rundunar ta ce ta kama waɗanda ake zargin kuma suna hannun ’yan sanda, yayin da bincike domin gano cikakken abin da ya faru da kuma ko akwai wasu mutane da ke da hannu a lamarin.
An ceto yaro ɗan shekara 9
A wani lamari kuma, rundunar ta ce jami’an Sashen Jakusko sun kama wani Muktar Haruna, mai shekaru 35, a ranar 1 ga watan Oktoba, 2026, bisa zargin cin zarafin yara.
Muktar, wanda ake zargin malamin Islamiyya ne, yana zaune a Garin Baduku, Ƙaramar Hukumar Jakusko.
Bincike ya nuna cewa ana zargin sa da ɗaure ƙafafun wani ɗalibi mai shekaru tara na tsawon kusan watanni huɗu.
Jami’an tsaro sun ceto yaron tare da kai shi Babban Asibitin Jakusko domin duba lafiyarsa.
Kwamishinan ’Yan Sandan Yobe, CP Usman Kanfani Jibrin, ya yi Allah-wadai da duk wani nau’in tashin hankali da cin zarafi, musamman a kan yara da sauran masu rauni.
Ya bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike kan lamarin, tare da tabbatar da cewa an bi matakan doka.
Rundunar ta kuma yi kira ga jama’a da su rik6a kai rahoton duk wani abun zargi tashin hankali ko aikata laifi ga jami’an tsaro.

