Mazauna karamar hukumar Jahun a jihar Jigawa na farin cikin dawowar wutar lantarki, bayan shafe shekaru 8 suna cikin duhu.
A zantawar mazauna yankin da Kamfanin Dillancin Labarai na NAN a ranar Litinin a Jigawa, sun ce, yaran da aka haifa ƙasa da shekara bakwai, ba su san me ake cewa wutar lantarki a yankinsu ba.
Wani ma’aikacin gwamnati a yankin Malam Muhammed Abdullah, ya bayyana godiyarsa ga sabon shugaban da ƙaramar hukumar bisa yadda wutar ta dawo ƙasa da wata guda da karɓar mulki.
Ya ce, “Mun yi mamakin dawowar wutar lantarki cikin gaggawa, kuma mun yaba da hangen nesa da shugaban ya yi, saboda rashin wutar lantarki ya kori ‘yan kasuwa da dama,”
- ‘Yan Najeriya Miliyan 14 Na Fama Da Cutar Sukari
- ICPC Za Ta Bibiyi Ayyuka 60 Da Suka Laƙume Miliyan Dubu 21 A Kaduna
Wani mai injin niƙa a Jahun Umar Baballe, ya ce rashin wutar lantarki ja tilasta masa haƙura da sana’ar.
Baballe ya ce da farko ya fara amfani da man dizal amma asara ya yi ta tafkawa.
Ya ce dawowar wutar lantarki ya inganta abubbuwa da yawa, hatta ruwan sha ya samu.
A nasa jawabin, shugaban karamar hukumar Jamilu Danmallam ya bayyana cewa daga hawansa kujerar mulkin karamar hukumar ne ya gayyaci masana da su binciki matsalar wutar lantarkin.
Ya ce baban abin da aka gano shine ɓata gari da ke lalata turakun wuta.
Danmallam ya ce, gano haka ne ya hada kai da ‘yan sanda da kungiyoyin agaji don magance matsalar, wanda hakan ya taimaka wurin dawowar wutar.
Danmallam ya yabawa Gwamna Umar Namadi bisa kasancewarsa nagartaccen jagora.