• Home  
  • An kama ɓarauniyar jariri a asibiti a Zamfara.
- Babban Labari

An kama ɓarauniyar jariri a asibiti a Zamfara.

An kama wata matashiya ’yar shekara 27, kan zargin satar jariri mai kwana 10 da haihuwa a Babban Asibitin Ƙaura Namoda da ke Jihar Zamfara. Dubun wadda ake zargin ya cika ne kwanan da sace jaririn, inda ’yan sanda suka fara gudanar da bincike bayan samun rahoton. Bayanan samun ƙorafin ne Babban Ofishin ’Yan Sanda […]

An kama wata matashiya ’yar shekara 27, kan zargin satar jariri mai kwana 10 da haihuwa a Babban Asibitin Ƙaura Namoda da ke Jihar Zamfara.

Dubun wadda ake zargin ya cika ne kwanan da sace jaririn, inda ’yan sanda suka fara gudanar da bincike bayan samun rahoton.

Bayanan samun ƙorafin ne Babban Ofishin ’Yan Sanda na Ƙaura Namoda, ya gayyaci jami’an asibitin da ke bakin aiki a lokacin da jaririn ya ɓace domin su amsa tambayoyi.

Kakakin rundunar, DSP Yazid Abubakar ya bayyana cewa jami’an sun taimaka da muhimman bayanai, “wanda ya kai ga gano jaririn a wata ruga mai suna Kogin Audu, daga Kaura Namoda.

“An yi nasarar ceto jaririn tare da kama wadda ake zargin ne sakamakon taimakawan da jama’a suka yi da muhimman bayanai.”

Ya ƙara da cewa an ceto jaririn cikin ƙoshin lafiya kuma an mika shi ga iyayensa. Ita wadda ake zargin kuma, mai suna Asmau Nasiru, tana tsare a hannun ’yan sanda inda take amsa tambayoyi.

DSP Yazid ya ruwaito Kwamishinan ’Yan Sanda na Jihar Zamfara, Ahmad Muhammad Bello ya yaba wa al’ummar jihar bisa yadda suka taimaka da bayanai a kan lokaci da ya kai ga ceto jaririn.

Ya kuma jaddada ƙudirin rundunar na ci gaba da aiki domin tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin jama’a tare da yaƙar ayyukan laifi a faɗin jihar.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000