Babbar kotun shari’ar musulunci dake zamanta a kasuwar kurmi Kano, ta bai wa mataimakin babban Sufetan ƴan sandan Nijeriya mai kula da shiyya ta ɗaya, ya binciki shugaban jam’iyar APC na jihar Kano, Abdullahi Abbas da kuma tsohon shugaban karamar hukumar Birnin Kano, Faizu Alfindiki, kan zarginsu da ɓata wa Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf suna.
Tun da fari dai Hon. Amir Abdullahi Kima, mai taimakawa gwamnan Kano a Ma’aikatar Shari’a da kuma Ishak Abdul Mataimakin Gwamnan kan fasahar zamani ne suka yi ƙararsu a kotun ƙarƙashin jagorancin mai Shari’a Abdu Abdullahi Wayya.
Kotun Kuma ta aike musu da sammaci amma wadanda ake karar basu bayyana ba, daga bisani suka turo lauyoyinsu tare da bayanin sukar hurumin kotu.
A zaman kotun na ranar Alhamis Mai Shari’ar ya tabbatar da hurumin kotun akan shariar, ya kuma umarci Ofishin ƴan sanda na shiya ta daya wato Zone One dake Kano kan su binciki waɗanda ake zargin, sannan su kawo su kotun domin fuskantar shari’ar.