An Kashe Mutane 7 A Filato

Akalla mutane bakwai ne aka kashe ciki har da wata mace daya a wasu hare-hare da aka kai a wasu kauyukan kananan hukumomin Bassa da Mangu a jihar Filato.

Majiyoyi sun ce kawo yanzu akwai mutane 12 da suka samu munanan raunuka, a halin yanzu suna karbar magani a asibitoci daban-daban.

Mazauna yankin sun ce harin na farko ya faru ne a kusa da yankin anguwar Ancha da ke karamar hukumar Bassa, yayin da na biyun ya faru a Gyenbwas Rinji da ke gundumar Langai a karamar hukumar Mangu.

Shugaban kungiyar ci gaban Fulani ta Gan Allah (GAFDAN) na Filato, Garba Abdullahi, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce an tabbatar da ɓatan makiyayan ne da karfe 3 na dare a lokacin da suke kiwon shanu, sai daga baya aka gano gawarwakinsu a unguwar Ancha.

“Makiyayan suna kiwo ne a lokacin da maharan suka ɗauke su daga wajen kiwo zuwa Ancha suka kashe su, mun kai rahoton lamarin ga ‘yan sanda da kuma ‘Operation Safe Haven,” in ji shugaban.

A Gyenbwas Rinji, an kashe mutane biyu da suka hada da mace guda, tare da kona gidaje da dama.

 

 

Post masu alaƙa

Gwamnatin Jigawa ta kashe kusan naira biliyan bakwai (7) domin tallafa wa ma’aikata ta fuskar noma

Jami’an tsaro sun ceto ɗalibai da malaman da aka sace a Kogi

Hukumomin tsaro sun kama wanda ya kirkiri hukumar bogi a Nijeriya