Hukumar kula da ilimi, kimiya da al’adu ta Majalisar Dinkin Duniya (UNESCO) ta ce a shekarar 2024 an kashe ‘yan jarida 68 a bakin aiki.
UNESCO ta bayyana cewa shekaru biyu a jere, rayuwar ‘yan jarida da ma’aikatan yada labarai na cikin mummunar hatsari a yankunan da ake fama da rikici.
Darakta Janar a UNESCO Audrey Azoulay ta bayyana cewa wannan shine karo na farko a cikin shekaru goma da aka salwantar da rayuwar ‘yan jarida a bakin aiki da dama haka.
Ta ce “Samun sahihan bayanai na da mahimmanci kwarai da gaske a duk lokacin da aka samu rikici, domin bayanan za su taimakawa jama’ar da abin ya shafa, kuma za a wayar da kan duniya baki daya.
“Bai kamata ‘yan jarida suna salwantar da rayuwar su a bakin aiki ba.
“Ina kira ga gwamnatoci su tashi tsaye wajen tabbatar da tsaron rayukan ‘yan jarida, bisa ga dokokin kasa da kasa.”
Rahoton na UNESCO ya ce an kashe ‘yan jarida 42 a yankunan da ake fama da rikici a bana, inda aka gano cewa an kashe ‘yan jarida 18 a Falasdinu.
Sauran ƙasashen kuma sune Ukraine, Kolombiya, Iraki, Lebanon, Myanmar, da Sudan.