Hukumar Lafiya Ta Duniya (WHO) ta bayyana cewa kaso 30 na masu mutuwa sakamakon zazzabin cizon sauro a duniya ‘yan Najeriya ne.
Rahoton da WHO ta fitar a ranar Alhamis ya ce Najeriya ita ma ta kai kusan kashi 40% na mace-macen zazzabin cizon sauro a fadin duniya a tsakanin yara ‘yan kasa da shekaru biyar.
A shekarar 2023 kaso 30.9% na wadan da zazzabin cizon sauro a duniya ‘yan Najeriya ne.
WHO ta bayyana cewa a duk duniya a shekarar 2023, an sami kusan mutane miliyan 263 ne aka kiyasta cewa sun kamu da cutar zazzabin cizon sauro.
Hukumar ta ce tsakanin shekarar 2000 zuwa 2019, adadin masu kamuwa da cutar zazzabin cizon sauro a kowace shekara ya karu kwarai da gaske.
A cewar rahoton na WHO, daga shekarar 2020, adadin masu kamuwa da cutar zazzabin cizon sauro ya karu sosai, inda kaso 89.7% na wadan da suka kamu da cutar suka fito daga Afirka.