Home » An Yi Girgiza A  Gwamnatin Kano

An Yi Girgiza A  Gwamnatin Kano

by Muhammad Auwal Suleiman
0 comment

Gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya sauke sakataran gwanatin jihar Dokta Abdullahi Baffa Bichi da shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin jihar Shehu Wada Sagagi an kuma sauke kwamishinoni 5.

Wannan na ƙunshe a cikin wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun daractan yaɗa labaran gwamnan na Kano Sunusi Bature Dawakin Tofa.

Baya ga haka gwamnan ya sauyawa mataimakinsa kwamared Aminu Abdulssalam ma’aikatar da yake lura da ita a matsayin kwamishina wato ta ƙananan hukumomi zuwa ma’aikatar ilmi mai zurfi.

Kwamishinonin da gwamnan ya sauke sun haɗa da kwamishinan yaɗa labarai Baba Halilu Dantiye da kwamishina a ma’aikatar kuɗi Ibrahim Jibril Fagge da kwamishinar al’adu da yawon buɗe ido Ladidi Ibrahim Garko da kwamishinan ayyuka na musamman Shehu Aliyu Yammedi da kwamishinan raya karkara Abbas Sani Abbas.

Gwamanan na Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya kuma sauyawa kusan dukkanin kwamishinonin jihar ma’aikatun da za su lura da su.

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai mai cikakkiyar rajista wadda manufarta ita ce ilimantarwa, da wayar da kai da Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.
Muna nan a kan titin Guda Abdullahi gida mai lamba 19 a Farm Centre, jihar Kano.

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi

©MuhasaTVR 2023. Ku nemi izini kafin yin amfani da duk abin da aka wallafa a wannan shafi

Are you sure want to unlock this post?
Unlock left : 0
Are you sure want to cancel subscription?