Ɗan majalisar wakilan Najeriya mai wakiltar Tsanyawa da Ghari a jihar Kano, Injiniya Sani Bala Tsanyawa ya tabbatar da sace mutane 18 a wasu ƙauyuka uku da ke yankin ƙaramar hukumar Tsanyawa.
Hon. Tsanyawa ya shaida wa BBC cewa ƴan bindigar sun shiga ƙauyukan uku a cikin daren ranar Talata ɗauke da makamai inda suka yi garkuwa da mutanen ciki har da mata.
Ya ƙara da cewa ƴanbingar na shiga ƙauyukan jihar ne daga jihar Katsina mai maƙwabtaka.
”Ƙauyukan da ƴan bindigar suka shiga sun haɗa da Biresawa, inda suka sace mutane biyar, sai ƙauyen Sundu da suka kama mutane huɗu, sai kuma ƙauyen Masaurari da suka kama mutane tara”, in ji ɗan majalisar.
Ya ci gaba da cewa a wasu lokuta ƴan bindigar kan shiga ƙauyukan a kan babura, a wasu lokutan ma ya ce a ƙafa suke shiga ƙauyukan.
Wani ɗan uwa ga waɗanda aka sace, Kabiru Usman, ya ce maharan sun zo ne a ƙafa ɗauke da makamai, suka kuma yi garkuwa da matarsa Umma, ɗiyarsa mai shekara 17, da matar ɗan’uwansa da wasu mata biyu daga Tsundu mai makwabtaka.
zuwa yanzu dai rundunar yan sandan Kano bata ce komai ba kan garkuwar da aka yi da wasu mutanen kauyen Biresawa a ranar litinin.
A baya-bayan nan jihar Kano ta fara fuskantar hare-haren ƴanbindiga daga iyakarta da Katsina, wani abu da masana ke alaƙantawa da sulhu da ƴanbindiga da ake yi a wasu ƙananan hukumomin Katsina.
