• Home  
  • Tinubu Ya Buƙaci Sojoji Su Killace Dazukan Kwara, Kebbi Da Neja
- Babban Labari - Labarai

Tinubu Ya Buƙaci Sojoji Su Killace Dazukan Kwara, Kebbi Da Neja

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya buƙaci, jami’an tsaron ƙasar su killace dazukan jihohin Kwara da Kebbi da kuma Neja, inda a baya-bayan nan ake samun ƙaruwar hare-hare tare da garkuwa da mutane. Cikin wata sanarwa da mai taimaka wa shugaban ƙasar kan harkokin yaɗa labarai, Sunday Daare ya wallafa a shafinsa na X, ya ce […]

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya buƙaci, jami’an tsaron ƙasar su killace dazukan jihohin Kwara da Kebbi da kuma Neja, inda a baya-bayan nan ake samun ƙaruwar hare-hare tare da garkuwa da mutane.

Cikin wata sanarwa da mai taimaka wa shugaban ƙasar kan harkokin yaɗa labarai, Sunday Daare ya wallafa a shafinsa na X, ya ce Tinubu ya buƙaci runsunar sojin saman ƙasar ta faɗaɗa sanya idanu ta sama kan dazukan, waɗanda ya yi imanin cewa nan ne mafakar yanbindigar.

Shugaba Tinubu ya buƙaci sojojin saman su faɗaɗa tsaron dazukan domin taimaka wa dakarun ƙasa.

A baya-bayan nan ne dai an samu garkuwa da ɗaliban a jihohin Kebbi da Neja da masu ibada a jihar Kwara

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai