An Ceto Daliban Da Yan Bindiga Suka Sace A Kebbi

Hukumomin Najeriya sun sanar da kuɓutar da ɗaliban Sakandiren ƴan mata da ke garin Maga a jihar Kebbi su 24.

Cikin wata sanarwa da kakakin shugaban shugaban ƙasar, Bayo Onanuga ya wallafa a shafinsa na X, ya ce Tinubu ya yi wa ɗaliban maraba da dawowa.

Shugaba Tinibu ya kuma ya yaba wa ƙoƙorin jami’an tsaron ƙasar kan kuɓutar da ɗaliban.

Wani bidiyo da aka wallafa na yaran bayan kuɓutar da su, wanda BBC ta gani ya nuna yaran cikin wata motar bas tare da jami’an tsaro, suna bayyana sunayensu ɗaya-bayan ɗaya.

Bidiyon ya kuma nuna yaran cikin murna da farin ciki yayin da suke tafiya a motar bas.

Shugaban Najeriya ya kuma yi kira ga jami’an tsaron ƙasar su ƙara ƙaimi domin ku butar da ragowar ɗaliban Neja da suka rage a hannun ƴanbindiga.

A makon da ya gabata ne wasu ƴanbindiga suka far wa makarantar tare da sace ɗalibai 25 da kashe malami guda.

Bayanan da ke fitowa daga yankin na cewa ɗaliban an kan hanyar zuwa Birnin Kebbi, fadar gwamnatin jihar.

Tun daga lokacin ne hukumomin ƙasar suka ɗauki matakai daban-daban domin kuɓutar da ɗaliban, daga ciki har da tura ƙaramin ministan tsaron ƙasar, Mohammed Bello Matawalle zuwa Kebbi domin ya kula da ƙoƙarin gwamnati na kuɓutar da ɗaliban.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *