An tsare ɗan takarar Shugabancin ƙasa a jam’iyyar African Action Congress {AAC}, Omoyole Sowore a ranar Lahadi, bayan dawowar sa daga ƙasar Amurka. An tsare Sowore ne a filin tashi da saukar jirage na Malam Aminu Kano, bayan dawowar sa daga ƙasar Amurka.
Sowore wanda ya bayyana hakan a shafinsa na X a safiyar ranar Lahadi, inda daga bisani yace an sake shi.
Jagoran juyin juya hali da kuma zanga-zanga Najeriya, ya bayyana cewa hukumomin shigi da fice na Najeriya sun karɓe fasfon sa, inda suka bayyana mai an basu umarnin su tsare shi.