Home » An Samar Da Fasahar Da Ke Satar Bayanan Sirri A Bankunan Najeriya-NITDA

An Samar Da Fasahar Da Ke Satar Bayanan Sirri A Bankunan Najeriya-NITDA

by Muhammad Auwal Suleiman
0 comment

Hukumar Bunkasa Fasahar Sadarwa ta Najeriya (NITDA) ta bayyana cewa akwai wata fasahar satar bayanan mutane a bankuna A Najeriya. 

NITDA ta yi wannan iƙirari ga ‘yan Najeriya game da fasahar “malware”, da ke satar bayanan masu mu’amala da da bankuna ne a ranar Litinin.

A cewar hukumar, sabuwar fasahar “Grandoreiro” babbar barazana ce, domin tana da damar iya sarrafa kwamfutoci da ke wurare daban-daban a lokaci guda.

NITDA ta tabbatar da cewa wannan fasahar na da ikon satar muhimman bayanai kamar bayanan banki da bayanan sirri.

Haka zalika NITDA ta bayyana cewa fasahar na da ikon tura saƙonnin bogi, kuma tana iya yaudarar mutane su cike takardun da ba sahihai ba.

NITDA ta yi gargaɗin cewa fasahar na iya haifar da asarar kuɗi da kuma muhimman bayanan sirri.

Hukumar ta bukaci jama’a su yi taka-tsan-tsan tare da ɗaukar matakan tsaro domin rage hadarin afkawa fasahar.

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai mai cikakkiyar rajista wadda manufarta ita ce ilimantarwa, da wayar da kai da Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.
Muna nan a kan titin Guda Abdullahi gida mai lamba 19 a Farm Centre, jihar Kano.

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi

©MuhasaTVR 2023. Ku nemi izini kafin yin amfani da duk abin da aka wallafa a wannan shafi

Are you sure want to unlock this post?
Unlock left : 0
Are you sure want to cancel subscription?