Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya ce jama’ar Arewacin Najeriya ba za su ragawa shugaba Tinubu ba a zaben 2027.
Atiku Abubakar, ya yi wannan bayanin a matsayin martani ga furucin Sakataren Gwamnatin Tarayya, Sanata George Akume, wanda ya ce ’yan Arewa su hakura da neman kujerar shguaban kasa a 2027, sai 2031 idan Tinubu ya kammala wa’adinsa na biyu.
An ruwaito George Akume na cewa ’yan Arewa ’yan Jam’iyyar APC mai mulki da ke son neman shugabancin kasa su hakura zuwa 2031.
A cewarsa, yanzu lokacin mulkin ’yan Kudu ne, don haka su jira sai Tinubu ya kammala wa’adinsa na biyu.
- An Samar Da Fasahar Da Ke Satar Bayanan Sirri A Bankunan Najeriya-NITDA
- Bam Ya Tashi Da Manomi A Neja
George Akume ya bukaci Atiku Abubakar, babban abokin hamayyar Tinubu a zaben 2023 daga babbar jam’iyyar adawa ta PDP ya hakura ya jira zaben 2031.
Atiku, ya bayyana cewa zabin shugaban kasa abu ne da ke hannun ’yan Nijeriya zu zabi wanda suke so.
Ya ce, kalaman Akume rashin adalci ne, domin a halin yanzu, ’yan Kudu sun mulki Nijeriya na tsawon shekara 17 takwas a karkashin Obasanjo, biyar a hannun Jonathan da kuma hudu a hannun Tinubu.
Atiku ya ce, idan aka kwatanta da ’yan Arewa da suka yi shekara 11, uku na Yar’Adua da takwas na Buhari.
Wannan martani ya fito ne ta hannun kakakinsa Atiku, Paul Ibe, in da ya ce bayanan Akume rashin adalci ne, yana mai bayyana cewa zabin shugaban kasa a hannun ’yan kasa yake.
Paul Ibe ya ce, ya kamata a tambayi Akume shin, “Me Gwamnatin Tinubu ta yi da ’yan Nijeriya za su kara zaben ta?”