Gwamnatin Jihar Filato ta sanya dokar hana fita na sa’o’i 48 a birnin Jos, bayan wani mummunan hari da aka kai a unguwar Rukuba da ke Ƙaramar Hukumar Jos ta Arewa a daren Lahadi.
Rahotanni sun bayyana cewa mutane da dama sun rasa rayukansu, yayin da wasu da dama suka jikkata a harin da wasu da ake zargin ’yan bindiga ne suka kai da misalin karfe 7:30 na dare.
Shaidu sun ce maharan sun kutsa cikin unguwar ne a bisa babura suna harbe-harbe ba kan mai uwa da wabi, lamarin da ya jefa al’umma cikin firgici.
Ba a iya tantance adadin waɗanda suka mutu ba a lokacin da aka kammala wannan rahoton ba.
Shaidu sun ce, bayan maharavan sun tsere daga unguwar, fusatattun matasa sun toshe hanya, tare da kai farmaki kan masu baburan Daidaita Sahu (Nape Riders) da fasinjojinsu.
Sojojin rundunar Operation Enduring Peace sun garzaya yankin domin dawo da zaman lafiya da kuma daƙile yaduwar rikicin.
Kakakin rundunar, Kyaftin Polycap Oteh, ya shaida wa wakilinmu cewa za su fitar da cikakken bayani bayan sun kammala bincike kan musabbabin harin. Sai dai a lokacin da aka kawo rahoton, bai fitar da ƙarin bayani ba.
A cikin wata sanarwa da Kwamishinar Yaɗa Labarai da Sadarwa ta jihar, Joyce Ramnap, ta fitar a ranar Lahadi, ta ce an ɗauki matakin ne domin daƙile yaɗuwar rikicin a Jos da kewaye.
Ta ce, “Sakamakon mummunan harin da ya faru a unguwar Gari Ya Waye, Anguwan Rukuba, a yau Lahadi 29 ga Maris, 2026, wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane da dama, tare da jikkatar wasu, Gwamnatin Jihar Filato tare da haɗin gwiwar hukumomin tsaro na sanar da kafa dokar hana fita na sa’o’i 48 a Ƙaramar Hukumar Jos ta Arewa, tun daga ƙarfe 12 na daren 29 ga Maris zuwa 1 ga Afrilu, 2026.”
Kwamishinar ta jajanta wa iyalan waɗanda abin ya shafa, tare da bayyana harin a matsayin “mummunan farmaki da ba a yi tsammani ba kan al’umma masu zaman lafiya,” inda ta tabbatar da cewa gwamnati na ɗaukar duk matakan da suka dace don kamo waɗanda suka aikata laifin.
Gwamnati ta buƙaci al’umma da su kwantar da hankalinsu, su kasance masu lura da tsaro, tare da bayar da duk wani bayani da zai taimaka wa hukumomin tsaro wajen gudanar da bincike.