Sheikh Pantami Ya Roƙi El-Rufai, Ribadu Da Uba Sani Su Sulhunta A Jana’izar Mahaifiyarsa

Sheikh Dr. Isa Pantami ya buƙaci Malam Nasir El-Rufai da abokan siyasarsa su ajiye saɓanin da ke tsakaninsu, ya yi wannan kiran ne a makabarta yayin binne mahaifiyar El-Rufai, Hajiya Umma, a Abuja.

Pantami ya yi wannan kira ne a huɗubarsa a maƙabartar Gudu ranar Lahadi. Ya roƙi shugabanni su fifita haɗin kai tare da tunawa da alherin da suka yi wa juna.

Ya jaddada cewa rayuwa mai wucewa ce kuma dole kowa ya bar duniya wata rana. Ya ƙara da cewa nasara na zuwa ne ta bin hanyar Allah ba dabarun siyasa ba.

A wurin jana’izar, manyan ‘yan siyasa da dama sun halarta ciki har da Uba Sani da Nuhu Ribadu. Haka kuma an gudanar da sallar jana’iza a Masallacin Ƙasa da ke Abuja.

Rahotanni sun ce mahaifiyar El-Rufai ta rasu a Masar ranar Juma’a. Lamarin ya zo yayin da yake fuskantar shari’a kan zargin kuɗaɗe a kotu.

Post masu alaƙa

PDP ce za ta lashe zaɓen 2027 a Jigawa — Sule Lamido

INEC ta bayyana dalilin cire wasu ’yan takarar gwamna daga jerin sunayen da ta fitar

Ƙungiyar agoya bayan  shugaba Tinubu a zargi yan Daba da hana ta kai tallafi ga marasa galihu a Bauchi .