Kotun kolin nijeriya ta tabbatar da sanata rufa’I sani hanga a matsayin zabbaben sanatan kano ta tsakiya a jam’iyar NNPP.
Kotun kolin bisa jagorancin mai shari’ah uwani abba aji, ta gudanar da hukuncin ne a yau jumu’ah , inda ta ayyana sanata rufa’I sani hanga a matsayin wanda ya lashe zaben na sanatan kano ta tsakiya a jami’iyar NNPP.
Da yake Karin haske game da hukuncin lauyan jami’iyyar ta NNPP barista Bashir tudun wazirci yace kotun kolin ta jaddada hukuncin baya na kotun tarraya .
Hukumar zabe mai zaman Kanta inec ta dai bayyana malam Ibrahim shekaru a matsayin wanada ya lashe zaben na sanatan kano ta tsakiya, lamarim da ya kawo cecekuce tsakanin yan jami’iyar ta NNPP.