Ana ci gaba da luguden wuta a biranen Khartoum da ma yankin yammacin Dafur a cewar shaidun gani da ido, duk da yunkurin kawo karshen rikicin da kasashen duniya ke yi.
Wani mummunan hari da aka kai ta sama a garin Ombada mai yar tazara da birnin Khartoum ya yi sanadiyar rayukan mutane 5 yayin da wasu 17 suka jikkata.
Masu aikin ceto na ci gaba da neman mutanen da suka makale a ɓaraguzan gine-gine lamarin da ya sa ake ganin adadin wadanda suka mutu ka iya karuwa.
Ya zuwa yanzu, sama da mutum dubu uku ne rikicin Sudan ya sa suka rasa rayukansu, a cewar wata kungiya mai tattara bayanan yaki.