Home » Mata Masu Juna Biyu Na Cigaba da Mutuwa a Arewa Ta Tsakiya – WHO

Mata Masu Juna Biyu Na Cigaba da Mutuwa a Arewa Ta Tsakiya – WHO

by Anas Dansalma
0 comment

Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce ana cigaba da samun matsalar mutuwar mata masu juna biyu a lokacin haihuwa jihohin Arewa ta tsakiya.

Hukumar dai ta ayyana jihar Neja cikin jihohin da ke fama da wannan matsala sasboda matsalar tsaro, duk kuwa da ƙoƙarin da jami’ai ke yi.

Hukumar ta ce da yawan yaran da aka haifa a wannan yankin ba a yi masu riga-kafi saboda yawan rikicin da ake samu masu alaƙa da rashin tsaro.

Shugabar da ke kula da shiyyar, Dr Asma’i Zeenat Kabir ce ta bayyana hakan a taron hukumar karo na 75 da ya gudana a Minna babban birnin jhar.

Hukumar ta yi kira kan hukumomi da su ƙara zage damtse don bunƙasa harkokin lafiya a yankin.

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai dake da cikakkiyar rejista da ke da manufa ta ilimantarwa, wayar da kai Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.

Ofishinmu yana nan a kan titin Guda Abdullahi dake Farm Centre a jihar Kano. 

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi