A yunkurinta na ceto ‘yan kasa daga kangin yunwa da samar da nagartaccen sakamako ta fuskar aikin gona,
Hukumar Bunƙasa Filayan Aikin Noma ta Ƙasa (NALDA) ta samar da makarantun horaswa ga manoma a jihohin Ogun, Katsina, Abiya da kuma Borno.
Wannan na kunshe cikin wata takarda wadda babban jami’in hukumar NALDA, Kaka Alhaji Mustapha ya rattabawa hannu tare da mika ta ga manema labarai.
Ya ce bayan shirye-shirye daba-daban da hukumar NALDA ke gudanarwa ga manoma mata da maza, yanzu kuma hukumar ta kafa makarantar da za ta rika bai wa su manoman horo a kan dabarun aikin noma yayin da su ma wadanda suka sami horon za su kware domin ganin an kai ga nasara a kan irin ayyukan da ita hukumar ta sanya a gaba.
Haka kuma ya kara da cewa samar da makarantun zai taimaka matuka wajan horas da manoma da kuma gudanar da duk wasu shirye-shirye wanda hukumar take yi cikin sauki, musamman wajen bai wa ‘yan sa- kai da sauran manoma bita a kan aikin gona.
Kaka ya ce makarantun za su gudanar da karatu a mataki na farko ne, za a fara ne da takardar shaidar difiloma a bangaran fannin aikin gona, sauran kwasa-kwasan sun hada da difiloma ta kimiyyan aikin gona da kiwo (Agricultural Technology & Animal Production) da kuma difiloma a kan kimiyar kiwon lafiya.