• Home  
  • Ana Shirin Kirkiro Jiha Guda Daga Kudancin Najeriya
- Babban Labari

Ana Shirin Kirkiro Jiha Guda Daga Kudancin Najeriya

An fara shirye-shiryen kirkiro jiha guda a Najeriya.

Dagin jihohin Najeriya

‘Dan majalisa Amobi Godwin Ogah mai wakiltar Isuikwuato/Umunneochi a jihar Abia tare da wasu ‘yan majalisa huɗu sun gabatar da ƙudurin ƙirƙiro ƙarin jiha guda a jihar Ekiti da ke yankin kudu maso gabashin Najeriya.

Kudurin da ‘yan majalisar suka gabatar ya tsallake karatu na farko a majalisar ranar Talata.

Ƙudurin na buƙatar a yi gyara a sashe na uku na kundin tsarin mulkin Najeriya, inda ya bukaci a goge lamba 36 a matsayin adadin jihohin Najeriya a maye gurbinta da lamba 37 don bai wa sabuwar jihar damar shiga jerin jihohin ƙasar. 

‘Yan majalisar sun bukaci a yanko sabuwar jihar daga jihohin yankin biyar. 

An ce sabuwar Jihar za ta ƙunshi ƙananan hukumomi 11, inda Lokpanta da a yanzu ke cikin jihar Abia, zai kasance babban birnin sabuwar jihar.

Ana sa ran kananan hukumomin da za su koma sabuwar jihar sun haɗa da Isuikwuato da Umu-Nneochi daga jihar Abia, da Orumba ta Arewa da Orumba ta kudu daga jihar Anambra, sai Ivo da Ohaozara jihar Ebonyi, da Aninri da Agwu da Oji River a jihar Enugu, da kuma Okigwe da Onuimo da ke jihar Imo.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai