Ministan Ilimi, farfesa Tahir Mamman, ya ce gwamnatin tarayya kadai ba za ta iya daukar nauyin ilimi ba a kasar nan.
Ministan ya bayyana hakan ne a yayin wani taron karramawa da aka shirya wa Dr. Emeka Offor da matarsa, Adaora Offor wadanda jami’ar Nsukka da jami’ar Nnamdi Azikiwe suka ba wa digirin girmamawa a kan fanin kasuwanci da fafutukar al’umma.
Ministan ya kara da cewa, gwamnati tana kashe kudade masu yawan gaske wajen daukar nauyin makarantu, inda ya ce akwai bukatar shigowar makarantu masu zaman kansu da kuma masu ba da taimako domin ganin an ciyar da ilimi gaba kamar yadda gidauniyar mista Offor ke yi.
Ya ce wannan zai karfafa wa gwamnati domin ba za ta iya daukar nauyin ilimi ba ita kadai ba.