Rundunar ƴan sandan Najeriya a jihar Jigawa ta ce an samu mummunan rikici tsakanin manoma da makiyaya a ƙaramar hukumar Birnin Kudu.
An ce lamarin ya yi sanadin mutuwar mutum biyu da ƙona wasu gidaje uku.
‘Yan sandan sun ce sun kama mutum biyar da hannu a afkuwar rikicin, inda ake ci gaba da gudanar da bincike a kansu.
Shaidun gani da ido sun bayyanawa manema labaru cewa makiyayan sun gayyato takwarorinsu daga jihar Katsina inda suka shiga yankin da shanunsu suka kuma lalata gonaki da dama.
- Ana Shirin Kirkiro Jiha Guda Daga Kudancin Najeriya
- Daukar nauyin ilimi ya fi karfin gwamnatin Tarayya-Ministan Ilimi na Najeriya
kakakin rundunar ƴan sanda a jihar Jigawa, DSP Lawan Shiisu Adam, ya ce jami’ansu da hadin gwiwa da jami’an hukumar tsaro ta civil defense da kuma ƴan vigilante sun kai ɗauki yankin, tare da tarwatsa masu rikicin.
Ya ce sun gano shanu 15 da aka gudu aka bari a wurin.
A cewarsa, rundunar ta aike jami’anta tare da ƴan vigilante domin tabbatar da zaman lafiya da hana ruruwar rikicin.