Hukumar Leƙen sirri ta Soji ta Najeriya (DIA) tana gudanar da bincike kan wani tsohon gwamna bisa zargin sa da ɗaukar nauyin sojoji da nufin yi wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu juyin mulki.
Majiyoyin Aminiya sun bayyana cewa akwai zargi mai karfi cewa tsohon gwamnan, wanda ɗan asalin yankin Kudu ne kuma tsohon babban jami’in gwamnati a ɓangaren albarkatun mai da iskar gas ne, ya ɗauki nauyin yunƙurin juyin mulkin, wanda da aka shirya aiwatarwa a ranar 25 ga watan Oktoban nan da muke ciki.
A ƙarshen mako ne kafofin watsa labarai na Shahara Reporters da Premium Times suka ruwaito cewa wasu hafsoshin soji 16, —waɗanda Hedikwatar Tsaro ta Najeriya ta ce sun shiga hannu saboda aikata abubuwan da saɓa ƙa’idar aiki— an tsare su ne saboda zargin su da yunƙurin kifar da Gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Daga cikin sojojin da aka kama akwai wani mai muƙamin Birgediya-Janar da wani Kanar da wasu na ƙasa da su da ke Ofishin Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara Kan Sha’anin Tsaro (ONSA).
Majiyar Aminiya ta tabbatar da cewa akwai ƙamshin gaskiya a rahoton zargin yunƙurin juyin mulkin.
Majiyar ta ce, “Gaskiya ne. Akwai hannun fararen hula, ciki har da wani tsohon gwamna, kuma ana bincike domin gano irin rawar da suka taka a ciki. A halin yanzu, sojoji 16 da ake zargi suna tsare.
Tsohon gwamnan da ke ake zargin tsohon mai babban muƙami ne a ɓangaren albarkatun mai da iskar gas, amma ba a riga an kai ga tabbatar da sa hannunsa a ciki ba.”
Wata majiyar kuma ta shaida mana cewa binciken na ƙoƙarin gano irin alaƙar da kuma tattunawar da ke tsakanin tsohon gwamnan da sojojin da aka kama.