Ana zargin wasu matasa da ba a gama tantance adadinsu ba, da farwa wasu mutane har cikin gidaje da sara da kuma jefe-jefe da Duwatsu, a unguwar Sheka dake karamar hukumar Kumbotso Kano.
Lamarin ya biyo bayan hana kidan Gangin Wani biki da masu ruwa da tsaki na unguwar Sheka suka hana yi don gudun tayar da fitina.
Wadanda ake zargin sun biyo matasan hanya lokacin da suke kan hanyar su ta zuwa gida, inda suka dinga saransu da makamai har suka ji musu munanan raunuka a sassan jikinsu.
Abdulkadir Auwal mai Shekaru 25, ya bayyana cewa sunje wajen kidan Gangin kuma tawo domin ance ba za a yi ba, suna cikin tafiya shida abokinsa mai suna Halifa Magaji, sai suka ji ana cewa gashi can shi za ku yiwa Rauni.
Ya kara da cewa juyawar da zai yi sai yaga sun yarda yaro daya kasa suna saransa da makamai, inda ya kai masa dauki amma suka rufe shi da duka da kuma Sara.
Sai dai ya ce dukkan matasan da suka far musu babu Wani abu da ya taba hada su na cacar baki domin baima sansu ba, sai lokacin da suka aikata musu ta’addancin yasan wuraren da suka fito.
” ni ban San kowa ba a cikin su Amma Wadanda Suka gansu sunce yan layin Danfodiyo ne dake Sheka ”.
A cewarsa sun sareshi akansa da Gwiwar hannu da Dan Yatsa da kuma suka da wata wuka a bayansa.
Halifa Magaji dan Shekaru 20, ya ce mutanen da suka tare su tare da samar musu raunuka sun hada da, Wani mai suna Dinga da Abban Faisal da Abdulwahabu da kuma Digi mai gyaran Takalmi.
Tuni Jami’an yan sandan Sheka suka shiga cikin lamarin bayan kai Wadanda aka samarwa da raunukan Asibiti.
Lamarin ya faru ne a ranar Lahadi da misalin karfe 12:30PM na Rana, lokacin da matasan suke kan hanyar su ta koma gida.
Sai dai Dagacin Sheka, Alhaji AbubaKar Musa Zakari, ya ce ba komai suke fada a Kafafen yada labarai ba, don haka bai yadda mun dauki muryarsa ba.
Sai dai ya ce, shida baturen yan sandan Sheka sun Kira wanda za a yi bikin Yar tasa kuma sun samu fahimtar junar cewar ba za a yi bikin ba Saboda wasu dalilai don wanzar da Zaman lafiya a yankin.
Ya kuma ce hatta mai Kidan Gangin Bai zo ba, domin an hana, Amma sun samu labari Mara dadi kan yadda aka farwa wasu matasa da Sara Har cikin gida, ya kuma tabbatar da cewa suna iya baking kokarinsu wajen ganin an hukunta duk wanda aka samu da Aikata laifi.
Abaya dai unguwar sheka an samu rigingimun matasa dake janyo rasa rayuka, Amma lamura sun lafa bayan Daukar matakan da masu ruwa da tsaki suke yi.