Daga: Mujahid Wada Musa
Kotun majistire mai Lamba 32 dake zaman ta a unguwar NormanSland ta ci gaba da sauraren shari’ar nan da ake tuhumar wasu matasa da laifin hadin baki, shiga ta laifi, aikata sata da fashi da makami da kuma siyan kayan sata, a garin Gurungawa dake karamar hukumar Kumbotso Kano.
A zaman kotun na ranar Alhamis an sake gabatar da Lawan Yakubu, Kabiru Garba, Usaini Hassan da Mubarak Basiru da tuhumar hadin baki, shiga ta laifi, aikata sata da kuma fashi da makami, wadanda tun abaya suka amsa laifinsu, kuma kotun ta ce a ci gaba da tsare su a gidan yari zuwa 8 ga watan Afrilun 2025.
Ana zargin su da addabar al’ummar garin Gurungawa, da satar Babura dauke da mugaggan makamai, inda mutanen garin suka kama su sannan suka mika su ga jami’an yan sanda, sannan suka gurfanar da su a gaban kotun.
Haka zalika, an karanto takaddar tuhumar da ake yi wa , Bashir Bello da mutane 2 wadanda basa gaban kotun, wato Najib Babura da kuma wani, da laifin hadin baki da siyan kayan sata, wanda ya saba da sashi na 97 da 317 na dokoki da hukunce-hukuncen laifukan arewacin Nigeria.
- Kotu A Kano Ta Yankewa Ƴan TikTok Biyu Hukuncin Zaman Gidan Yari
- Ƙungiyar Ƴan tawayen M23 Na Cigaba Da Kai Hare-Hare A Yankin Gabashin Congo
Wanda ake tuhuma na farko da siyan Baburin sata Bashir Bello, ya amsa laifinsa.
Tunda fari ana zarginsa da siyan wani Babur da aka sato a garin Gurungawa mai kimar kudi naira miliyan daya da dubu dari daya mallakar Abdullahi Bala, inda ake zargin Bashir Bello ya siya kan kudi naira dubu dari da sittin.
Lauyar gwamnatin jihar Kano, Barista Saima, ta roki kotun ta yanke masa hukunci nan ta ke , amma kotun ta ce ‘’ duk laifin da aka aikata ya kai shekaru uku wajibi ne a ji bangaren shari’ar ta hanyar gabatar da shaidun abubuwan da ake tuhumar musu da aikatawa’’.
Lauyan da ke kare Bashir Bello , ya roki kotun ta sanya shi a hannun beli karkashin sashi na 35 da na 36 na kundin tsarin tsarin mulkin Nigeria na shekarar 1999 wanda aka yi wa gyaran fuska.
Kotun karkashin jagorancin mai shari’a , A’isha Abdullahi Waiya, ta bayar da umarnin tsare shi a gidan a jiya da gyaran hali da tarbiya har zuwa ranar 11 ga watan Maris 2025.