Daga Shareef Khalifa Sharifai
Mayakan M23 sun kai sumame asibitin CBCA da asibitin Heal Africa a daren Ranar 28 ga watan Fabrairu, inda suka yi awon gaba da marasa lafiya 116 da wasu 15, A cewar mai Magana da yawun ofishin kare hakkin Dan Adam na Majalisar Dinkin Duniya, Ravina Shamdasani.
Ana kyautata zaton mazajen da aka dauke dakarun Jamhuriyar Demokradiyyar Congo ne ko kuma manbobin wata kungiyar dake marawa gwamnatin baya da ake kira Wazalendo.
Shamdasani ta ce, akwai takaici matuka ganin yadda kungiyar mayakan M23 ke sace marasa lafiya daga gadajen asibiti, A Guraren da ake tsare Dasu a kuma rike su ba tare da basu damar yin magana da kowa ba a wuraren da ba wanda ya sani, inda ta yi kiran da a gaggauta sakin su.
- Gwamnatin Kano Ta Ƙaddamar Da Rabon Abincin Buɗa-Baki
- Shugaba Tinubu Ya Bada Umurnin Kammala Titin Abuja Zuwa Kano
Masu magana da yawun kungiyar mayakan ta M23 Willy Ngoma da Lawrence Kanyuka Kingston basu ce uffan ba a nan take, a lokacin da aka nemi jin ta bakin su.
Kungiyar kabilar Tutsi mai jagorantar kungiyar ta M23 ta yi tattaki har cikin birnin Goma a karshen watan Janairu, kuma tun daga nan ne suka yi nasarar nausawa cikin Gabashin Congo, suka kwace yankuna da samun iko kan muhimman albarkatun karkashin kasa.
Cigaba da nausawar, wadda ta somo a karshen watan Disamba, tuni ta yi muni wajen rincabewar rikici data yadu zuwa cikin Congo na irin kisan kiyashin da aka yi a Rwanda a shekarar 1994, da fadi tashin da ake yi na samun iko kan dimbin albarkatun karkashin kasa a Congo.
Congo da kwararru a Majalisar Dinkin Duniya da manyan kasashen yammaci duk sun zargi Rwanda da mara bayan kungiyar ‘yan tawayen.