Home » An kama yan Bindiga 4 dauke muggan makamai A Kano

An kama yan Bindiga 4 dauke muggan makamai A Kano

by Mujahid Wada Guringawa
0 comment

 

 

Rundunar yan sandan jihar Kano, ta samu nasarar kama wasu mutane hudu da ake kyuatata zaton yan bindiga ne, dauke da makamai da kuma kudi , a kan titin By pass dake unguwar Hotoro karamar hukumar Nasarawa ta jihar.

Kakakin rundunar yan sandan jihar SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne tabbatar da hakan da yammacin asabar, inda ya ce ‘’ jami’ansu ne dake aiki a ofishin yan sanda na Jarkuka,  karkashin jagorancin SP Ahmed Abdullahi ne suka samu nasarar kama su, bayan samun bayanan sirri kan yunkurinsu na shigowa jihar don siyan bindiga kirar AK47.

Wadanda rundunar ta kama sun hada da Shukurana Salihu mai shekaru 25, Rabi’u Dahiru dan shekaru 35, Ya’u Idris mai shekaru 30 dukkansu mazauna jihar Katsina da kuma Muktar Sani mai shekaru 30 mazaunin unguwar Yandodo Hotoro Kano.

Ana Zargin Wasu Matasa Da Sayen Mashin Ɗin Miliyan 1 Kan Dubu 160

Kotu A Kano Ta Yankewa Ƴan TikTok Biyu Hukuncin Zaman Gidan Yari

SP Abdullahi Kiyawa, ya kara da cewa nasarar ta samu ne kamar yadda babban sifeton yan sanda na kasa IGP Kayode Edeolu Egbetokun, yaba su umarnin tabbatar da an kara fadada sintiri a lungu da sako don tabbatar da tsaro a fadin Nigeria.

Rundunar ta kama wadanda ake zargin ne a ranar 6 ga watan Maris 2025, da misalin karfe 2:00PM na rana a yunkurinsu na siyan bindigar a cewar SP Abdullahi Haruna Kiyawa.

An samu bindigu kirar gida guda 3, harsasai daban-daban guda 12, kwanson harsashi 4, Adda 1, Wukake 4 da Boris  guda 24, wayoyi 4, sai kuma kudi naira miliyan daya da dubu ashirin da takwas da dari takwas do za su sayi bindiga kirar AK47 da su.

Haka zalika rundunar ta tabbatar da cewa yanzu haka ta fara gudanar bincike akansu kuma da zarar ta kamala za ta gurfanar da su a gaban kotu don su fuskanci hukunci.

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai mai cikakkiyar rajista wadda manufarta ita ce ilimantarwa, da wayar da kai da Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.
Muna nan a kan titin Guda Abdullahi gida mai lamba 19 a Farm Centre, jihar Kano.

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi

©MuhasaTVR 2023. Ku nemi izini kafin yin amfani da duk abin da aka wallafa a wannan shafi

Are you sure want to unlock this post?
Unlock left : 0
Are you sure want to cancel subscription?