Jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya za ta gudanar da zaɓen fitar da gwanin takarar shugaban ƙasa a gobe Asabar ta hanyar ƴartinƙe.
Cikin wata sanarwa da jam’iyyar ta fitar ta ce za a gudanar da zaɓukan a faɗin mazaɓun ƙasar 8,809.
Shugaba Tinubu da Stanley Osifo ne ke neman tikitin tsayawa jam’iyyar takara a zaɓen 2027.
Jam’iyyar ta ce duk wanda ke da katin rajistar jam’iyyar na da damar zaɓar wanda zai yi wa jam’iyyar takara.
Sanarwar ta ce za a tattara sakamakon zaɓukan kowace mazaɓa a ƙaramar hukuma, kafin akai shi babban cibiyar tattara sakamakon ta ƙasa da ke Abuja.
Jam’iyyar ta kuma naɗa tsohon shugaban majalisar dattawan ƙasar, Sanata Pius Anyim Pius a matsayin shugaban kwamitin zaɓen fitar da gwanin shugaban ƙasar.
Yayin da ta naɗa Sanata Ali Ndume a matsayin shugaban kwamitin ƙarɓar ƙorafe-ƙorafen zaɓen.

