Tsohon mataimakin shugaban Najeriya Atiku Abubakar ya yi kira ga hukumar zaɓe mai zaman kanta da ta gaggauta sake duba ranar da aka tsayar domin gudanar da babban zaɓe na 2027, yana mai cewa lokacin ya yi karo da azumin watan Ramadan.
A ranar Juma’a INEC ta sanar cewa za a gudanar da zaɓen shugaban ƙasa da na ƴan majalisun tarayya a ranar 20 ga watan Fabrairu, 2027, yayin da za a gudanar da zaɓen gwamnoni da na ƴan majalisun jihohi a ranar 6 ga watan Maris, 2027.
Da yake mayar da martani a cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X, Atiku ya ce ranar 20 ga Fabrairu ta faɗo “a tsakiyar watan Ramadan,” yana mai bayyana lokacin a matsayin na gudanar da azumi da ibada ga miliyoyin Musulmin Najeriya.
“Sanya lokacin gudanar da wannan muhimmin al’amari na jama’a a tsakiyar lokacin ibada yana nuna rashin fahimta da rashin kulawa ga al’amuran zamantakewa da addini na ƙasar,” in ji sanarwar.
Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya ƙara da cewa yana da mauƙar muhimmanci a yi la’akari da yadda Najeriya ta ƙushi al’ummomi daban-daban kafin a yanke shawarar da za ta shafi rayuwar ƴan ƙasar.
A nata ɓangaren hukuma zaɓe mai zaman kanta (INEC) ta bayyana cewa an zaɓi ranakun zaɓen ne bisa la’akari da tanade-tanaden kundin tsarin mulki na 1999.

