admin

Shugaban Hukumar Aikin Hajji Na Kasa ya yi murabus

Shugubaban Hukumar Aikin Hajji ta Kasa (NAHCON) Farfesa Abdullahi Usman Saleh, ya yi murabus daga kujerarsa. A daren Litinin din nan Aminiya ta samu labarin ajiye mukamin Farfesa Abdullahi Usman Saleh, a daidai da hukumar ke tsaka da shirin gudanar da aikin Hajji na wannan shekarar. Wani jami’i a hukumar ya bayyana cewa ajiye aikin […]

Read more

Tinubu za mu zaba a 2027 —Sheikh Jingir

Fitaccen malamin Musulunci, Sheikh Muhammad Sani Yahaya Jingir, ya bayyana cewa Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ne zabinsu a babban zabe na 2027. Sheikh Jingir, wanda shi ne Shugaban Majalisar Malamai na Kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa Ikamatis Sunnah (JIBWIS) ya bayyana zabin Tinubu ne a yayin taron kara wa juna sani na shekarar 2026 […]

Read more

Ana zanga-zanga kan dokar gyaran zaɓe a Najeriya

An fara zanga-zanga a Abuja, babban birnin tarayya, yayin da jam’iyyun adawa da ƙungiyoyin farar hula da ƙungiyoyin kwadago ke zargin Majalisar Tarayya da tauye dimokuraɗiyya ta hanyar ƙin amincewa da ƙudirin da zai wajabta tura sakamakon zaɓe ta na’ura. Zanga-zangar ta ɓarke ne bayan da ‘yan majalisa suka ƙi amincewa da wani sashe na […]

Read more

Saudiyya za ta zuba jarin biliyoyin Dala a Siriya

Saudiyya ta sanar da wani gagarumin zuba jari a fannin samar da ababen more rayuwa a Syria, a yayin da ta ke jaddada goyon bayanta ga gwamnatin Damascus. Ƙasar Saudiyyar ta sanya kuɗin da ya kai dala biliyan biyu wajen gina sabbin filayen tashi da saukar jirage biyu a birnin Aleppo, da kuma dala biliyan […]

Read more

Shettima ya kai ziyara Kwara bayan mummunan harin jihar

Mataimakin shugaban Najeriya, Kashim Shettima ya kai ziyarar jaje zuwa jihar Kwara inda mahara suka kashe gomman mutane cikin makon nan. Cikin wata sanarwa da fadarsa ta fitar ta ce Shettima ya kai ziyarar ce bisa umarnin shugaban ƙasar Bola Tinubu. “Shugaban ƙasa, Bola Tinubu ya umarci mataimakinsa ya kai ziyarar jaje jihar da kuma […]

Read more

APC ta naɗa Masari shugaban babban taronta na ƙasa

Jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya ta maye gurbin gwamnan jihar Imo Hope Uzodinma da tsohon gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari a matsayin shugaban kwamitin babban taronta na ƙasa. Babban sakataren jam’iyyar na ƙasa, Surajudeen Basiru ne ya bayyana haka cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X. Jam’iyyar ta saka ranakun 27 […]

Read more